1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan Jamus a Chadi ya dawo gida

April 10, 2023

Sa'o'i 48 gwamnatin mulkin soji ta kasar ta ba jakadan na Jamus da ya tarkata kayansa ya bar kasar bayan zargin cin fuska ga kasar ta Chadi da hukumomi suka zargi jakadan da aikatawa.

https://p.dw.com/p/4PsRe
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Jakadan Jamus wanda kasar Chadi ta kora daga kasarta Jan-Christian Gordon Kricke ya dawo nan gida Jamus, inda ya sauka fadar gwamnati da ke birnin Berlin. Kafin barin da ya yi wa birnin N'Djamena ba tare da cikakkiyar shiryawa ba sai dai sauran jakadan kasashen ketare da ke Chadi suka yi masa rakiya zuwa filin jirgin sama, a wani mataki na nuna damuwarsu ga abin da ya faru da shi.

Sa'o'i 48 gwamnatin mulkin soji ta kasar ta ba jakadan na Jamus da ya tarkata kayansa ya bar kasar bayan zargin cin fuska ga kasar ta Chadi da hukumomi suka zargi jakadan da aikatawa. A cikin sanarwar da suka fitar sun ce dabi'un jami'in diflomasiyyar na Jamus sun yi hannun riga da yarjejeniyar birnin Vienna da aka kulla a kan diflomasiyyar kasashen duniya.

Sai dai rahotanni na cewa korar da aka yi masa ba ta rasa nasaba da sukar gwamnatin rikon kwarya ta sojoji da jakadan ya rika yi a baya-bayan nan. Amma kawo yanzu Ofishin kula da harkokin ketare na Jamus ya ce ya fara magana da gwamnatin Chadi a kan wannan al'amari.