Batutuwan tsaro sun sa 'yan Najeriya cikin dimuwa
November 30, 2020Batun rashin tsaro kusan za’a ce shi ne yafi daukar hankalin ‘yan Najeriya a lokacin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi yakin neman zabensa, inda mafi yawa sun zabe shi ne cike da fatan ganin zai shawo kan matsalar. Shekaru biyar a kan karagar mulki da Shugaba Buhari ya yi har yanzu Najeriyar na fama da wannan matsala. Bisa lakari da abubuwan da suka faru a karshen mako a jihar Borno ko za’a ce har yanzu akwai sauran rina a kaba game da alkawulan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya daukar wa al'ummar kasar a yayin yakin neman zabensa a cewar masu sharhi kan harkokin siyasar Najeriya irin su Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa ne da ke jami’ar Abuja.
Karin Bayani: Ana rayuwa cikin fargaba a yankin arewacin Najeriya
Kallo ya koma kan 'yan majalisa
Sanin cewa ‘yan majalisa sun kasance masu wakiltar jama’a kuma in abubuwa suka lalace su ake nunawa ‘yar yatsa, to ko me suke yi na ganin an shawo kan matsalar da ke zama gwama jiya da yau, Hon Mansur Ali Mashi dan majalisar tarayya ya ce majalisar dokokin kasar na iyakar kokarinta domin ganin an inganta fannin tsaro da ke cikin wani mawuyacin hali a Najeriya.
Karin Bayani: An samu yawaitar kananan makamai a Najeriya
A baya gwamnatin ta sha ikirarin cewa ta murkushe ko kuma ma ta ragen karfin ‘ya'yan kungiyar Boko Haram, da ma yunkurin kawo karshen tashin hankali, sai dai ga abubuwan da ke faruwa ‘yan Najeriya na koken gwamnati bata hobasa ba yadda suke bukata, duk da yake gwamnati na ci gaba da zartar da matsayinta na cewa tana matukar kokari wajen magance matsalolin tsaro.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan da aka yi a jihar Borno, ‘yan Najeriya na addu'o'in samu mafita daga wannan matsala ta rashin tsaro da ta addabi Najeriya ta kuma bazu zuwa wasu kasashen Afirka makwaftan kasar.