1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sultan: Ana rayuwa cikin fargaba a arewacin Najeriya

November 27, 2020

A karon farko sarakunan gargajiya sun bayyana damuwa kan halin rashin tsaro da yankin arewacin Najeriyar yake ciki duba da tsawwalar hare-haren 'yan ta'adda da masu garkuwa da jama'a.

https://p.dw.com/p/3lveZ
Nigeria Abuja Sultan  Sokoto Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar IIIHoto: DW/N. Mahaman Kanta

Ga dukkan alamu tura ta kai bango kan batun rashin tsaro a tarayyar Najeriya bayan ya dauki hankalin sarakunan kasar irin su Sultan Sa'adu Abubakar  da ke zaman sarki mafi tasiri a sashen arewacin Najeriya inda ya ce yankin na Arewa na daukacin mamayar 'yan ina da kisa masu cin karensu ba babbaka.

Karin Bayani: Yawaitar kananan makamai a Najeriya

Sultan Sa'ad ya ce babu kasuwa ba wani kauye da masu aikata ayyukan ta'addanci ba su ratsawa a yankunan arewacin Najeriya, yana mai bayyana irin girman annobar ta 'yan bindiga da  kuma kamarin da matsalar tsaro  ke kara yi a Najeriya, wacce sarakuna da ma talakawan kasar na yankin Arewa ke cewa hakan na kan hanyar rusa daukacin kasar, a cewar Murtala Aliyu sakataren kungiyar dattawan arewacin Najeriya ACF.

Karin Bayani: Buhari ya magantu kan batun tsaro

Nigeria - Boko Haram Konflikt
Sojojin Najeriya a fagen yaki da Boko HaramHoto: picture alliance/dpa

Kalaman basaraken na zuwa ne a daidai lokacin da wani rahoto cibiyar kula da ta'addanci ta duniya ke fadin har yanzu Najeriyar na zama ta uku mafi fuskantar annobar 'yan ta'adda a duniya. Kasa da sa'o'i 24 da suka gabata 'yan bindiga sun halaka wani basaraken gargajiya a Jihar Ondo, a ci gaba da hari da satar al'umma da na tabarbarewar tsaro a Arewa maso gabashin Najeriya  da ma daukacin sassan arewacin kasar.