1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Sarkin Musulmi Sa'adu Abubakar

July 15, 2010

A matsayinsa na Sarkin Musulmi shi ne jagoran al'uman Musulmi miliyan fiye da 60 dake Najeriya

https://p.dw.com/p/OMkT
Tsohon ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier tare da Sultan na Sokoto, Muhammadu Saadu AbubakarHoto: picture-alliance/ dpa
An dai haifi Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'adu Abubakar ne a ranar 24 ga watan Augustan shekarar 1956 a birnin Sokoto dake Arewacin Najeriya, kuma shi ne Sultan na 20 a ƙarƙashin daular Usmaniya.

A matsayinsa na Sarkin Musulmi shi ne jagoran al'uman Musulmi miliyan fiye da 60 dake Najeriya. A ranar 2 ga watan Nuwanba ne dai Alhaji Sa'adu Abubakar ya gaji wansa marigayi Mohammadu Macciɗo Sultan na 19 wanda kuma ya rasu sakamakon wani hatsarin Jirgin saman kanfanin ADC jim kaɗan bayan tashinsa daga filin Jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Sa'adu Abubakar dai shi ma ya kasance ɗa ga Sultan na 17, Saddiq Abubakar Usumanu wanda ya shafe shekaru fiye da hamsin akan karagar mulki. Sultan Sa'adu ya shiga aikin Soji a shekarar 1975, kuma bayan ya kammala horon Sojin ne ya zama laftana wato mai anini ɗaya. Bayan wannan kuma Sarkin Musulmin ya halarci kwasa-kwasai a ciki da wajen Najeriya a ƙasashe da suka haɗa da Indiya da Kanada.

Bayan komowarsa gida ya zama kwamandan Sojojin Tankan Soji masu bada kariya ga shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1980. Bayan wannan kuma ya zama kwamandan dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar OAU a Chadi. Har ila yau Sarkin Musulmin ya zama wakilin Soji na Najeriya a ƙungiyar Ecowas, bayan zama wakili a rundunar Sojin yammacin Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Saliyo.

Kafin naɗa shi Sarkin Musulmi na 20, Sa'adu Abubakar ya zama wakilin Sojin Najeriya a ofishin Jakadancin Najeriya a Pakistan. Kuma yanzu haka yana da matar Aure da kuma 'ya'ya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Ahmad Tijani Lawal