1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Jihohi na son agajin kudi don inganta tsaro

August 12, 2020

A yayin da ake ci gaba da kokarin samun mafita dangane da rashin tsaro a Najeriya jihohin kasar 36 sunce suna bukatar dauki daga gwamnatin tsakiya da nufin tunkafrar matsalar tsaro da ke barazana ga makomar al'umma.

https://p.dw.com/p/3grNm
Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency

Duk da cewa gwamnatin tarayya ce ke da hurumin tafiyar da ayyukan tsaro da suka shafi 'yan sanda da sojoji da sauransu gwamnatocin jihohin Najeriya na neman taimakon gwamnatin tarayya don magance matsalolin tsaro da ke abbadar sassa dabam-daban na Najeriya.

A yayin wata ganawa da shugaban kasa jihohin 36 na Najeriya sun nuna tsananin bukatar samun agaji daga gwamnatin tsakiya don warware matsalolin tsaro biyo bayan tabbatar da cewa suna kashe makudan kudade kowane wata don dafawa jami'an tsaronsu na ganin sun tattabar da tsaron al'umma, a yayin da a share daya matsalar annobar Covid-19 ta yiwa tattalin arzikinsu kisan gwani.

Gwamnonin jihohin na cewa wadannan jerin matsaloli na kara durkusar da tattalin arzikinsu da kuma hana su samun kudaden shiga batun da kakakin gwamnatin tarayyar Najeriya Malam garba Shehu "ya ce hadin kai a yanzu tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi ya zaman wajibi a kokarin da bangarorin ke yi na ganin sun tabbatar da tsaro da kare lafiyar al'umma." Kafin wannan a lokuttan baya wasu jihohin sun sha zargin jami'an tsaron tarayyar Najeriya da gazawa wajen tabbatar da tsaro al'umma, wanda har ta kai ga wasu jihohin da dama samar da rundunonin sa kai da nufin ganin an kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar yankunan Najeriya.

Shi kansa gwamnan Borno kuma jagoran yakin rashin tsaron a kwanakin baya ya zargi rundunar sojojin kasar da kitsa wani harin da yake zargin na neman ransa ne, ko da yake ga masu sharhi kan tattalin arzikin Najeriya ire-irensu Bashir Ibrahim na mai ganin cewa "akwai bukatar sauyin taku da kuma sabbin dubaru daga bangaren jihohi da mafi yawansu hankalinsu ke a kan duk wani kokari na inganta rayuwar al'umma da tabbatar da tsaro." Abin jira a gani a yanz shi ne tasirin da sabon tsarin zai yi a kokarin tabbatar da tsaron da ya kwashe kusan rabin dukiyar Najeriya kuma har yanzu kasar ta kasa samun kwanciyar hankali.