1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afirka ta Kudu na tsaka mai wuya

December 2, 2022

Wani bincike ne dai ya gano yadda aka sace wasu makudan kudade a gonar shugaban kasar Afirka ta Kudu lamarin da ya janyo rikicin da ke neman kai kujerarsa kasa, inda ake ta kiraye-kirayen da ya sauka daga mulki.

https://p.dw.com/p/4KOP0
Birtaniya, London | Cyril Ramaphosa Shugaban Afirka ta Kudu
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta KuduHoto: Wiktor Szymanowicz/AA/picture alliance

Majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudun ce ta kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa karkashin jagorancin tsohon alkalin alkalai Sandile Ngcobo, domin binciko yadda aka yi aka gano dala miliyan hudu a gonar  Phala Phala mallakin Shugaba Cyril Ramaphosa a shekarar 2020. Zargin dai da ake yi wa shugaban, wani babban saba doka ne da ke iya zame wa kujerar Mr. Ramaphosa gagarumar barazana.

Ba a dai kai ga ayyana cewa ya aikata laifi ba ya zuwa yanzu, amma kuma masu nazarin lamarin na cewa sakamakon na iya shafarsa da jam'iyyar ANC da ma kasar baki daya.

Cyril Ramaphosa, Shugaban Afirka ta Kudu
Kiraye-kiraye sun yi yawa na Cyril Ramaphosa ya yi murabusHoto: Justin Tallis/AFP/Getty Images

Kundin tsarin mulkin Afirka ta Kudu dai ya ce abubuwa uku ne ke iya sanya a tsige shugaban kasa, wadanda suka hada da karya doka mai karfi ko aikata ba wani daidan ba da kuma gazawa wajen iya gudanar da ayyuka da suke wajibi shi ne zai yi su. Kuma kwamitin binciken ya ce Shugaba Ramaphosa ya aikata biyu daga cikin laifukan.

Richard Calland, Farfesa ne a kan dokokin da suka shafi ayyukan gwamnati a jami'ar birnin Cape Town, ya ce tabbas makomar shugaban kasar na tangal-tangal. Tuni dai jam'iyyun siyasa suka yi nisa wajen kira ga Shugaba Ramaphosa da ya yi murabus. Amma kuma jagoran jam'iyyar Democratic Alliance, John Steenhuisen ya ce da sauran rina cikin kaba, ganin cewa aiwatar da sakamakon bincike na iya shafar kasar Afirka ta Kudun ne baki daya.

Binciken dai ya fito ne makonni uku gabanin babban taron jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudun, inda Shugaba Ramaphosa ke gaba-gaba daga cikin wadanda ke neman takarar shugabancin kasar.

Nkosazana Dlamini-Zuma
Shugabar ANC, Nkosazana Dlamini-Zuma, lokacin wani babban taron jam'iyyar a birnin JohannesburgHoto: picture-alliance/Zumapress/D. Naicker

Amma kuma an jiyo shugaban jam'iyyar Nkosazana Dlamini Zuma na kiran Shugaba Ramaphosa da kawai ya yi murabus. Sai dai kakakin jam'iyyar Pule Mabe, ya ce kwamitin gudanarwar jam'iyyar zai bayyana matsayinsa kan mataki na gaba.

Majalisar dokokin Afirka ta Kudun dai ta shirya muhawara kan sakamakon binciken ne a ranar Talatar makon gobe, kuma idan har aka rinjayi batun, lallai shugaban kasar zai fuskanci matsala, yayin da a gefe guda ofishin Shugaba Cyril Ramaphosa, ke cewa yana nazarin rahoton binciken kuma zai bayyana matsayinsa a lokacin da ya dace.