1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a bincike shugaban Afirka ta Kudu

Abdourahamane Hassane
November 30, 2022

Shugaban Afirka ta Kudu Ciryl Ramaphosa na cikin halin tsaka mai wuya gabannin makwannin biyu a gudanar da muhiiman zabuka a kasar.

https://p.dw.com/p/4KISa
Südafrika I Cyril Ramaphos I Untersuchung zu Korruptionsvorwürfen
Hoto: Rodger Bosch/AFP

Hakan ya biyo bayan yadda wani kwamitin ya mika rahotonsa ga majalisar dokoki a kan zargin da ake yi wa shugaban da boye wani lamarin ba tare da shaida wa 'yan sanda ba. Na wasu makudan kudade sama da miliyan uku na Euro da 'yan fashi suka taras a boye a wani gidan gonarsa da ke a wajen Johanesburg tun a shekara ta 2020. Majalisar dokokin kasar ta Afirka ta Kudu za ta yi muhawara a kan batun a ranar Tala mai zuwa, wanda ka iya sa a kada kuri'ar tsige shugaban kasar. Ko da yake ma jam'iyyarsa ta ANC na da rinjaye a majalisar. Ramaphoza wanda ya gaji Jacob Zuma wanda da ka tilasta masa yin marabus a shekara ta 2018 saboda zargin cin hanci wanda ake tsare da shi a gidan kurkuku ya yi watsi da zargin, yana mai cewa lallai barayin sun taras da kudaden a gonarsa amma yawansu bai kai yadda aka byyana ba.