Kujerar Ramaphosa na ashirin kufcewa
December 1, 2022Rahotanni sun nunar da cewa batun karya dokokin cin-hancin, na da nasaba da gidan gona mallakar Shugaba Cyril Ramaphosa. Tun da fari dai tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Arthur Fraser ne ya bayyana cewa, Ramaphosa ya yi kokarin boye makudan kudin da aka gano a gonar tasa a shekara ta 2020. Koda yake tuni Ramaphosa ya bayyana cewa, kudin da aka sata dalar Amirka dubu 580 kacal ba miliyan hudu da Fraser ya yi zargi ba.
Haka kuma Ramaphosa ya musanta zargin yana da hannu a satar kudin, inda ya ce ba shi da masaniya a kansu. Tuni dai 'ya'yan jam'iyyar adawa da ma wasu daga jam'iyyarsa African National Congress ANC mai mulki, suka shiga cikin masu kiransa da ya sauka. A na sa ran shugabannin jam'iyyar ANC mai mulkin, za su yi wata ganawar gaggawa kan makomar Shugaba Ramaphosa.