Najeriya: Guterres ya kai ziyara Borno
May 3, 2022Yayin ziyarar tasa a jihar ta Borno da ke zaman makyankyasar 'yan ta'addan Boko Haram masu gwagwarmaya da makamai a Najeriya, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya fara ganawa da 'yan gudun hijira ne da ta'addancin Boko Haram din ya tarwatsa. Rahotanni sun nunar da cewa, 'yan gudun hijirar sun yi matukar nuna jin dadinsu da ziyarar ta Guterres. Daga bisani Antonio Guterres din ya isa fadar gwamnatin ta Borno, inda wakilinmu na jihar Al-Amin Suleiman Muhammad ya ruwaito cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya bukaci Majalisar Dinkin Duniyar ta taimaka masa a kokarin da gwamnatinsa ke yi na mayar da 'yan gudun hijirar garuruwansu na asali. Tun bayan bullar kungiyar 'yan ta'addan ta Boko Haram a Najeriya dai, dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren ta'addanci da suke fuskanta daga kunyar, baya ga wadanda suka halaka da kuma wadanda suka asace suke tsare da su har kawo yanzu.