Guterres: Bukatar taimaka wa Nijar
May 2, 2022Jamhuriyar Nijar din dai, na fama da tarin matsalolin tsaro da na sauyin yanayi da ke ci gaba da yi wa kasar illa. A nasa bangaren yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da António Guterres din, shugaban Jamhuriyar ta Nijar Mohamed Bazoum ya nunar da cewa ta'addanci ya tilasta kasar kara yawan sojoji da kuma ba su horo fiye da a baya da kuma samar musu da sababbin kayan aiki. A cewarsa hakan na lakumewa Nijar makudan kudi a daidai lokacin da matsalolin sauyin yanayi ke ci gaba da yi wa kasar illa. A ranar Laraba ne dai António Guterres zai tashi zuwa yankin Oullam na jihar Tillaberi mai fama da matsalolin tsaro da talauci, domin tattaunawar kai tsaye da al'ummar yankin dangane da halin da suke ciki da kuma taimakon da suke fatan samu daga Majalisar ta Dinkin Duniya.