Jamus za ta taimaka wa yankin Sahel
April 15, 2022Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta jagoranci wata lakca a jami’ar birnin Yamai na jamhuriyyar Nijar, kan batun alakar da ke da akwai tsakanin matsalar sauyin yanayi, da ta karancin abinci da kuma ta tsaro a yankin Sahel da kuma gudunmawar da Jamus za ta iya kawo wa kasashen na Sahel wajen shawo kan wadannan matsaloli.
Ministar harkokin wajen kasar ta Jamus Baerbock wacce ta soma wata ziyarar aiki ta kwanaki a kasar ta Nijar, ta kwashe kusan awa daya tana gabatar da bayani a gaban daruruwan dalibai da malaman jami’ar birnin Yamai kan matsalar sauyin yanayi da kuma alakar da ke da akwai tsakanin wannan matsala da ta karancin abinci da ma ta tsaro a yankin na Sahel.
Kazalika ta kuma yi bayani kan irin rawar da Jamus ke takawa a cikin wannan kokowa a Sahel inda amma ta bayyana bukatar hada karfi da karfi domin tunkarar matsalar sauyin yanayi wacce ta ce ita tushen sauran matsalolin.
Ta ce, ''Mun gani kuma mun ji zahirin wannan matsala ta sauyin yanayi a wannan yanki, mun fahimci kuma alhakin da ke kanmu da wajen da ya haifar da wannan matsala, shi ya sa muka fara karfafa hulda da kasashen yankin a fannin yaki da sauyin yanayi da kuma samar da makamashi, amma maganin matsalar shi ne, ba yakar matsalar ba akan takarda, mu dage ya kasance a zahiri kuma yana daga cikin muhimman matakai na magance matsalar sauyin yanayi''
A wannan Alhamis ministar harkokin wajen kasar ta Jamus za ta kai ziyara a Ouallam cikin Jihar Tillabery inda za ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Mali dana Nijar kafin da yamma ta halarci taron manema labarai hadin gwiwa da takwaranta na Nijar ta kuma karkare da ganawa da Shugaban Mohamed Bazoum a fadarsa.