Sabuwar makoma ga Jamus a yankin Sahel
April 13, 2022Kasashen Afirka guda biyu ne ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baebock za ta yada Zango a yankin yammacin Afirka. Mali da kuma janhuriyar Nijar. Kasashen biyu na fama da matsalolin tsaro. Za ta gana da shugabannin gwamnati a biranen Bamako da Niamey, tare da kai wa sojojin kasa da kasa na MINUSMA da EUTM ziyara.
Makomar rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr a Malin na daga cikin muhimman batutuwa da za ta tattauna, kasancewa wa'adinsu a Mali na karewa a watan Mayu. An samu koma bayan danganta tsakanin gwamnatin mulkin sojin Mali da tarayyar Turai a watannin baya bayan nan, sakamakon ci gaba da dage lokutan mayar da kasar kan tafarkin dimukuradiyya da kuma alakar da ke tsakaninsu da sojojin Rasha.
Tun a tsakiyar watan Maris ne dai Faransa ta sanar da janye dakrunta da ke yaki da masu tada kayar bayan na Mali. Yanzu kuma ana cigaba da mahawara a nan Jamus dangane da ko akwai bukatar sojojin Jamus din su ci gaba da zama a Mali, wadanda ke kasar tun shekara ta 2013 inda suke aikin bada horo ga jami'an tsaron Malin. Ulf Laessing kwararre ne kan yankin Sahel a gidauniyar Konrad Adenauer.
"Hakika ya dace mu tattauna kan tsawon lokacin da muke son ci gaba da zama a Mali, ko manufofinmu na aiki, ko me za mu iya ingantawa, amma zan yi gargadi game da janyewar ba zato ba tsammani, kamar yadda muka yi a Afganistan. Janyewar za ta kara tsananta matsalolin tsaro a Mali kuma ya baiwa Rasha dama."
To sai dai duk da wannan damuwa, a ranar Litinin kungiyar tarayyar Turai ta dakatar da aikin bayar da horo a Mali. Bayan ganawarsa da ministocin harkokin wajen Turan a Brussel, jami'in kula da harkokin kasashen ketare na EU Josep Borrell ya ce, wannan matakin kadai ya haifar da illa ga rundunar sojin wannan kasa ta Afirka. A hirasa da tashar DW mai sharhi kan Nijar Seidick Abba ya ce akwai bukatar la'akari da wasu bangarori.
"Ba za a iya yakin da sojoji kadai ba. Akwai bukatar saka hannun jari wajen inganta rayuwar jama'a da makomarsu, misali a fannin horar da matasa sana'o'i. Ba wai kawai a tsaya ga sayen jirage masu saukar ungulu na yaki ko kara yawan sojoji a cikin rundunar ba. Bugu da kari dole ne a koma ga tushen matsalar tare da kawar da wuraren ta'addanci a yankin Sahel. A wannan fanni ne kasa kamar Jamus za ta iya taimaka wa Nijar."
Akwai sojojin Jamus 300 a bangaren rundunar Turai da ke horar da sojojin Mali da ake kira EUTM a takaice. Kazalika ta na da wasu jami'an soji 1,000 a bangaren shirin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na MINUSMA. Kuma wa'adin zaman rundunonin biyu a Mali, zai kare nan da makonni, idan har majalisar dokoki ta Bundestag ta amince.