1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za mu aika da wakili zuwa Sudan - Guterres

May 1, 2023

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres zai aika da babban jami'i zuwa arewa maso gabashin Afirka sakamakon rikicin nan da ke faruwa a Sudan.

https://p.dw.com/p/4Qk40
Hoto: FEISAL OMAR/REUTERS

Shugaban hukumar kula da jinkai Martin Griffiths, zai tashi ne zuwa Sudan cikin gaggawa, saboda yadda halin da ake ciki a Sudan din ke ci gaba da tabarbarewa, a cewar Guterres.

Ya zuwa yanzu dai sama da mutum 500 ne suka mutu a Sudan cikin makonni uku da barkewar rikicin.

Bangarorin na Sudan dai sun sake amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku karo na uku, abin kuma da bai kai ga burge 'yan kasar ba saboda rashin gani wani sassauci a wadanda aka yi a baya.

Hukumar samar da abinci ta duniya ta yi gargadin cewa rikicin na iya jefa yankin gabashin Afirka cikin sabuwar matsala ta jinkai.

Tuni ma dai farashin kayyayaki suka fara tashi a kasashen Chadi da Sudan ta Kudu, wadanda duk ke fuskantar karuwar kwararar 'yan gudun hijira daga Sudan.