1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Rasha sun kame 'yan adawa 263

Abdul-raheem Hassan
November 5, 2017

Sama da masu zanga-zanga 200 ne ke tsare a ofishin 'yan sanda, bayan da suka yi dandazon nuna adawa da salon shugancin shugaba Vladimir Putin a tsakiyar birnin Moscow.

https://p.dw.com/p/2n3g9
Russland Moskau - Demonstration zum Tag der Einheit des Volkes
Hoto: Getty Images/AFP/M. Zmeyev

Mai fafutika a kasar Rasha Vyacheslav Maltsev, ya kirayi magoya bayan sa ta shafin sa na internet da su fito gangamin kalubalantar shugaba Putin. Wasu rahotanni daga kasar sun ruwaito cewa yawancin masu zanga-zangar da aka tsare, suna dauke da wukake da kananan bindigogi masu amfani da harsasan roba.

To sai dai a wata sanarwa da rundunar 'yan sanda suka fitar, na cewa sun tsare mutanen ne bisa laifin gudanar da zanga-zanaga ba bisa ka ida ba. An dai saba fito na fito tsakanin jami'an 'yan sanda da 'yan adawa a Rasha, inda ko watan Yunin da ta gabata an tsare mutane sama da 1,500 da suka amsa kiran madugun 'yan adawar kasar Navalny da ke caccakar jami'an gwamnatin kasar kan cin hanci.'Yan sandan Moscow sun kama jagoran Adawa