1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Moscow sun kama jagoran Adawa

Abdul-raheem Hassan
June 12, 2017

Jami'an tsaro a kasar Rasha sun kama jagoran zanga-zanaga Alexei Navalny sa'o'i kalilan gabannin fara gangamin nuna adawa da karuwar cin hanci da rashawa a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/2eX17
Russland Proteste in Moskau
Hoto: Reuters/S. Karpukhin

Duk da garkame jagoran an samu halartar masu bore sama da 1,000 a kan titunan kasar, sanye da kaya masu launi dauke man'yan allunan, inda aka yi musu rubutun Allah wadai da 'yan siyasa da ke karban cin hanci. Kafofin yanar gizo da ke sa ido a kan al'amuran siyasar Rasha, na cewa 'yan sanda sun kuma yi awon gaba da wasu rukunin masu tattakin. Dama dai hukumomin tsaro sun haramta gudanar da zanga-zanagar a babban cibiyar taron kasar da ke birnin Moscow.

Alexie Navalny na ci gaba da samun tagommashi a bangaren adawa, wanda ake gani zai kalubalanci shugaban kasar Viladmir Putin, a babban zaben kasar na shakera ta 2018. To sai dai Navalny ya shiga gidan yari har na tsawon kwanaki bakwai, bayan da ya jagoranci wata zanga-zanga mafi girma a watan Maris din bana, inda ya danganta ayyukan rashawa da wasu man'yan 'yan siyasar kasar.