1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama dalibai masu goyon bayan Falasdinawa a Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 1, 2024

'Yan sandan dai sun fara kama daliban ne da karfe 9 na daren Talata, suna jefa su cikin motoci, yayin da wasu daliban ke yi wa 'yan sandan ihu.

https://p.dw.com/p/4fNpb
Hoto: Kena Betancur/AFP/Getty Images

'Yan sandan birnin New York din Amurka sun kama tarin daliban jami'ar Columbia, bayan sun yi dandazo tare da gudanar jerin gwanon zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinwa da ke fuskantar hare-haren Isra'ila.

karin bayani:Gwamnatin Amurka na son masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa su yi bore cikin lumana

'Yan sandan dai sun fara kama daliban ne da karfe 9 na daren Talata, suna jefa su cikin motoci, yayin da wasu daliban ke yi wa 'yan sandan ihu. 

Karin bayani:Dan bindiga ya kashe mutum uku a Amirka

Shugabar Jami'ar Minouche Shafik, ta bukaci 'yan sandan su ci gaba da zama a harabar jami'ar har zuwa ranar 17 ga wannan wata na Mayu, don tabbatar da tsaro da zaman lafiya, a daidai lokacin da ake shirin bikin yaye dalibai nan da 'yan kwanaki.