Dan bindiga ya harbe dalibai a jami'ar Las Vegas
December 7, 2023Hukumomin yankin sun tabbatar da mutuwar akalla mutum uku a wani hari da wani dan bindiga dadi da ya kai kan wasu daliban jami'a a Les Vegas da ke kudu maso yammacin kasar.
Tuni dai jami'an 'yan sanda suka hallaka mutumin domin dakile ci gaba da harbin kan mai uwa-da-wabi a jami'ar Nevada da ke jihar da ta yi kaurin suna wajen hare-haren 'yan bindiga.
Hukumomi ba su tabbatar da wasu bayanai game da maharin ba tukuna, amma wasu bayanai da manema labarai suka tattara sun gano cewa mutumin dan shekaru 67 ne kuma tsohon Farfesa da ke karantarwa a jami'o'in Georgia da North Carolina.
Shugaban Amirka Joe Biden ya nuna takaicinsa kan ayyukan 'yan bindaga dadi dake kai farmaki a jami'o'i da kwalejojijjn dake kasar. Harbe-harben bindaga ya zama ruwan dare a Amurka, kasar da ke da yawan bindigogi fiye da yawan al'ummarta.