2025: Fatan al'ummar Nijar
January 1, 2025Talla
Wannan shekara dai da ta yi bankwana ta 2024, shekara ce wadda a cikinta al'umma a Jamhuriyar Nijar ta kasan ce cikin yanayi na kangin rayuwa inda radadin takunkumi da aka kakaba wa kasar ya hadu da matsaloli na rayuwa. Wanda duniya ke fama da shi wanda duk da juriya da al'umma ta nuna mutane sun ji a jikinsu musamman ma dangane da tsadar rayuwa.
Koma da yake daga bisani hukumomi sun dauki matakai na kawo sassauci a fannin kiwon lafiya, man fetur, da rangwame na siminti sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta haddasa babbar barna a sassa dabam-dabam na kasar. Sai dai kuma al'umar ta Nijar na cike da fata a wannan sabuwar shekara ta 2025.