Sharhi:Takun saka Nijar da Najeriya
December 27, 2024Bayan da Janar Abdourahamane Tiani ya kwaci mulki a hannun gwamnatin dimukaradiyya ta Mohamed Bazoum, ya kasance ba mai karfin gaba inda ya dinga fuskantar alkiblar da yake so ba tare da shayin kowa ba. Hasali ma, ya yi ta kai ruwa rana da uwar gijiyar Jamhuriyar NIjar wato Faransa har ma sauran kasashen Yamma, kuma ya ga bayansu, da sunan samar wa kasarsa farcen susa ta hanyar juya babin mulkin mallaka kwata-kwata. Dadin dadawa ma dai, jagoran mulkin sojan Nijar ya toshe kunnuwarsa ga gargadin kungiyar ECOWAS na maida mulki ga zababbiyar gwamnati ko kuma ta yi amfani da tsinin bindiga wajen kawar da shi. A wannan marra ma ya ci gari, saboda kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta mai da wukarta cikin kube.
Abin tambaya a nan shi ne, da wane saddabaru Janar Tiani ya yi amfani wajen biyar da maza tare da karfafa mulkinsa? A fili yake cewar gwamnatin mulkin sojan Nijar ta yi amfani da mafarkin 'yan kasa na ganin cewar Faransa ta daina tafiyar da akalar mulki da arzikinsu na ma'aidin uranium a fakaice, lamarin da ya sa kaso mai yawa na 'yan Nijar musamman ma matasa da suka rasa ayyukan yi suka yi ta sam-barka. Sannan al'ummar arewacin Najeriya sun tabbatar da abin da mawaki ke fadi cewar "abin da ya taba hanci, idanu ruwa suke yi", inda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin cewar shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya da ECOWAS ya lashe amansa. Wannan ya nuna irin mutunci da 'yan uwantaka da ke tsakanin Danjuma da Dan-Jummai wato Najeiya da Nijar. Sai dai a yanzu, ba a iya tantance inda Janar Abdourahamane Tiani ya dosa ba, saboda ya zama damusar takarda da ke tsoro da kuma ke ban tsoro. Ya kai ga raba wasu masu hamayya da gwamnatinsa da takardunsu na 'yan kasa wai da sunan cin amanar kasa duk da cewar Nijar kasa ce ta iyaye da kakanni. Amma, anya uba na iya rungumar wasu daga cikin 'ya'yansa saboda suna gari ne, sannan ya mayar da wasu saniyar ware saboda yana daukansu a matsayin baragurbi? Wannan abin dubawa ne.
Babban tashin hankila ma dai, shi ne yadda gwamnatin mulkin sojan Nijar ke nuna irin wannan halaya da makwabtanta. Janar Abdourahamane Tiani ya mayar da kasashen Mali da Burkina Faso abin amincewa saboda dodo daya suke yi wa tsafi, lamarin da ya sa su hada gwiwa wajen kafa kawancen AES da ke ba su damar magana da murya guda tare da mayar da su tsintsiya madaurinki daya. A daya hannun kuma, bayan yunkurin raba gari da kungiyar ECOWAS, ya dauki karar tsana ya dora wa Jamhuriyar Benin da Najeriya, inda yake zarginsu da zama 'yan amshin Shatan Faransa duk da karyatawa da suka sha yi. A takaicen-takaicewa dai, Janar Tiani ya mayar da zarge-zargen neman kai wa Nijar hari a matsayin garkuwar mulkinsa.
To me abin yi domin Nijar ta magance sabaninta da makwabta da kyautata tafiyarta? To gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sani cewar har yanzu ruwa bai kare wa dan kada ba. Akwai damammaki da yawa a gabanta na daidaita turbar da ta dora kasar da al'umar NIjar a kai. Tunda sulhu alhairi ne, akwai bukatar Janar Tiani ya wakilta jami'ai ko kuma ya nika gari domin zuwa kasashe makwabta da yake samun sabani da su domin fahimtar juna da bude sabon babin dangantaka tsakaninsu. Sannan Tiani ya zauna da sauran shugabannin AES wato Assimi Goita na Mali da Ibrahim Traoré na Burkina Faso domin gindaya ka'idojin komawa cikin dangi na ECOWAS domin magana da murya guda, ko kuma su shata dangantaka da za a samu tsakanin kawancen AES da ECOWAS domin guje wa komabayan da wannan rabuwa za ta jawo. Idan ba haka rabuwa tsakanin bangarorin biyu, zai zama tamkar haihuwar guzuma, da kwance, uwa kwance.