1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun mutu a tsare a Chadi

April 19, 2020

Wasu da ake zarginsu da zama 'yan kungiyar Boko Haram sun rasa rayukansu a Chadi yayin da suke tsare a gidan yarin N'Djamena babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3b8w4
Mali Unruhen l Erneuter Angriff auf Soldaten - Symbolbild
Hoto: Umago/Belga/N. Maeterlinck

Hukumomin a Chadin sun tabbatar da mutuwar mayakan na Boko Haram su 44, wadanda suka kasance cikin 'yan bindiga 58 da aka kama lokacin wani sintiri na musamman da dakarun kasar suka kaddamar a baya-bayan nan a dazukan yankin.

Ana dai ci da bincike kan yadda aka yi mayakan tarzomar suka mutu, koda yake wasu masu bincike sun nunar da ce ta yiwu watsa musu wata iska mai guba aka yi, wadda ta haddasa musu hardewar zuciya da kuma numfashi.

Dama hukumomin sun ce a ranar Alhamis da ke tafe ne za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Ranar 31 ga watan Maris da ya gabata ne dakarun Chadi suka kaddamar da hare-hare kan mayakan Boko Haram a maboyarsu, aikin da suka kwashe akalla mako guda suna yi.

Hare-haren sun kuma yi sanadin mutuwar mayakan na Boko Haram akalla dubu guda yayin da Chadin ta rasa sojojinta 52.