1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tanzaniya: 'Yan adawa na tsoron dawowar salon mulkin danniya

Zainab Mohammed Abubakar
August 13, 2024

An bayar da belin shugaban babbar jam'iyyar adawa ta kasar Tanzania Chadema, kamar yadda kakakin jam'iyyar ya bayyana, bayan da aka tsare su gabanin wani gangamin ranar matasa.

https://p.dw.com/p/4jQ3s
Jagoran adawa Freeman MboweHoto: Michael Jameson/AFP/Getty Images

Kimanin mutane 520 ne aka kama a fadin kasar, a cewar sanarwar ‘yan sanda, gabanin haramtacciyar zanga-zangar Chadema a jiya Litinin, wanda aka sa ran zai janyo dubban matasa a birnin Mbeya da ke Kudu maso Yammacin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da masu adawa da gwamnati sun fara nuna fargabar cewar, matakin da 'yan sandan suka dauka na iya nuna komawa ga tsarin zalunci na tsohon shugaban Tanzaniya John Magufuli.

Kamen dai ya zo ne duk da furucin shugabar da ta gaje shi Samia Suluhu Hassan, wadda ta sha alwashin komawa fagen siyasa tare da sassauta wasu takunkuman da aka yi wa 'yan adawa da kafafen yada labarai, ciki har da dage haramcin taron 'yan adawa na tsawon shekaru shida.