An harbi fitaccen dan adawa a Tanzaniya
September 7, 2017Rahotanni daga kasar Tanzaniya na cewa wasu mutane da ba a kai ga tantance ko su wane ne ba sun kai hari da bindiga a gidan mataimakin madugun 'yan adawar kasar Tundu Lissu inda suka jikatashi.
A cikin wata sanarwa da jam'iyyarsa ta Chadema ta fitar a wannan Alhamis ta ce an harbi mataimakin shugaban nata a ciki da kuma a kafa kuma yanzu haka an garzaya da shi zuwa assibiti rai kwakwai mutu kwakwai.
Tundu Lissu wanda dan majalisar dokoki ne a kasar ta Tanzaniya dan siyasa ne da ya yi fice wajen sukar lamirin Shugaban kasar tasu John Magufuli. Kuma an kai masa harin ne a da misalin karfe biyu agogon GMT a gidansa da ke a birnin Dodoma babban birnin kasar jim kadan bayan dawowarsa daga zaman majalisa.
Hukumar 'yan sandar birnin na Dodoma ta sanar da soma gudanar da bincike kan wannan batu.