1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin neman zaben a Najeriya

Aliyu Abdullahi Imam
November 22, 2018

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da yakin neman zabensa tare da yi wa 'yan Najeriya alkawarin daukar kasar zuwa mataki na gaba. Yayin da Atiku Abubakar ya yi alkawari na bunkasa tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/38ipt
Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Hoto: Atiku Media Office

Atiku Abubakar dai ya sha alwashi na bunkasa harkar zuba jari a fannin mai da rage tallafi da rubanya tattalin arzikin Najeriyar nan da 2025 muddin ya yi nasara a zaben na 2019. Ya ce zuba jarin zai sanya a samar wa mutane miliyan biyu da rabi aiki a tsame akalla mutane miliyan 50 daga cikin talauci. Matakan da gwamnatin Buhari ta ce ta yi nisa a kansu.