Buhari da Atiku na neman hanyoyin nasara a 2019
October 8, 2018Nasarar da tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ta ‘yan adawa ya samu, bayan da ya kayar da mutane 11 da suka yi takara, ya nuna cewar shi ne ke kalubalantar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki. Wannan ya bude sabon babi a guguwar siyasar da ke kadawa, domin kar-ta- san- kar a tsakanin mutanen guda biyu.
Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja ya bayyana hasashensa ga irin fafatawar da za'a yi, inda ya ce " Za'a yi fafatawa mai zafin gaske ganin cewar Atiku Abubakar hamshakin dan siyasa ne da kuma wanda yake yi wa adawa shugaban kasa da ke rike da madafun iko."
Alamu na nuna cewar za'a kai ga kartar kasa a tsakanin jam'iyyun biyu a kokari na kaiwa ga madafun iko, duk da rashin dama ta amfani da bangaranci ko addini, Abin da ya sanya Dr Usman Mohammed masanin kimiyyar siyasa a Abuja ya ce ya kamata a yi taka tsantsan.
Bayanai na nuna cewar manyan 'yan takara da Atiku Abubakar ya samu nasara a kansu irin su gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya koma don karbar tikitin gwamnan a PDP, yayin da Sanata Rabiu Musa kwankwaso da Bukola Saraki suka koma don takarar Sanata a mazabansu na Kwara da Kano. Amma ga Isa Tafida Mafindi kwararen dan siyasa ya ce 'yan takara neman shugabancin Najeriyar fa sun san juna.
Al'ummar Najeriya na cike da fata ta samun sauyi a wannan takara da za'a fafata a tsakanin mutanen biyu da kowa ke jin shi kwararre a fagen siyasar Najeriyar.