WHO ta yi gargadi kan zuzuta cutar Corona
February 3, 2020Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, WHO, ta ce tana aiki ka’in da na’in da kamfanonin sadarwar Intanet saboda yaki da karairayin da wasu ke yadawa dangane da cutar nan ta coronavirus da ta addabi China da wasu kasashen duniya.
Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadi kan hadarin da ke tattare da yada labarai marar tushe game da cutar, wadda a yanzu ta hallaka rayukan sama da 360 a China.
Wannan matsayi na WHO, na zuwa ne daidai lokacin da China ke zargin Amirka da zuzuta matsalar, da kuma ke tayar da hankali a duniya.
A wannan Litinin ne kuma hukumomi a Wuhan na China inda cutar ta bulla, suka kaddamar da wani sabon asibiti da aka gina cikin kwanaki 10, musamman saboda kula da wadanda ke fama da wannan cuta.
Sama da mutum dubu 17 da 300 ne dai suka kamu da cutar a kasar ta China, yayin kuma da ake da wasu daidaiku a wasu kasanshen.