Wariyar launin fata da talauci ne matsalolin baki a Jamus
May 8, 2024Hakika matsalar wariyar launin fata ta yadu a Jamus. Amma wane sakamako na zahiri za ta iya haifarwa ga wadanda abin ya shafa? Klara Podkowik, masaniya da ke cibiyar nazarin ala'amuran baki da sajewarsu cikin al'umma ta duba irin wadanda lamari ya shafa, inda ta duba ko akwai alaka tsakanin wariyar da ake nunawa da kuma talauci. Ta ce: "Kusan 20% na matan Musulmai da muka zanta da su tun daga shekarar 2013 ne suka zo Jamus. Sun shigo ne daga Siriya da Afghanistan da sauran kasashe. Kuma an riga an san cewa 'yan gudun hijirar na fuskantar barazanar talauci saboda wahalar shiga sahun wadanda za a dauka aiki”.
Karin bayani: Talauci a Jamus
Tushen nazarin shi ne Hukumar Kula da Wariyar Jama'a ta kasa wanda Salikutluk ta dauki nauyin gudanarwa. Kamar yadda masaniyar ta ce: "Idan aka yi la'akari da kididdigar hukuma ko rahoton talauci da arzikin da gwamnatin tarayyar Jamus ke samu, yawancin talauci ya fi ritsawa da mutanen da ke da asalin hijira a kasar ta Jamus. Kuma wannan ya shafi har da wadanda suka samu takardun zama dan kasa kasa.”
Karin bayani:Masallatai a Jamus na fuskantar barazana
Binciken da aka yi ya gano cewa akasarin baki a Jamus ba wai basu da ilimi b ane, misali 33% mutanen da aka tambaya musamman Musulmi na da ilimin da ake bukata ko kuma sun kware a wanni fanni, amma sun fuskantar matsala wajen neman aiki, domin wasu jami'o'i da makarantun gaba da sakandare na kasar Jamus ba sa la'akari da shaidar karatun. A cewar Klara Podkowik, "Mutanen da ke da sunan Turkawa misali, suna da karancin damar gayyatar su zuwa bitar inda ake daukar aiki. Kuma tabbas wadannan bangarorin y akakmata a yi gyara a kai”
Karin bayani: Jamus: Cusa dokokin Musulumci a siyasa
Amma akwai bukatar samun ilimi a kasa ta asali da mutum ya fito don zai hanzarta shigar 'yan gudun hijira da sauran 'yan ci-rani cikin kasuwar kwadago ta Jamus. A wani bangaren kuma, wadanda suka yi karatu gabanin zuwansu kasar Jamus sun fi saurin koyon harshen Jamusanci, wanda ke zama babbar dama ta samun aiki cikin sauri.