Armutsbericht Deutschland
May 20, 2008
GwamnatinTarayya Jamus ta bayyana rahoto agame da yanayin talauci da kuma jama´ar dake fama da shi a wannan ƙasa.
A jiya ne ministan ƙwadago a gwamnatin Tarayya Olaf Scholz ya gabatar da wanan rahoto ,wanda ya bitar halin da Jamus ke ciki a game da talauci.
Duk da ƙarfin tattalin arzikin da akewa Jamus kirari, rahoton ya ce ko wane mutum ɗaya, daga jerin mutane takwas na fama da fatara da talauci a ƙasar Jamus.
idan aka cire tallafin da gwamnatin Tarayya ke baiwa marasa aikin yi wannan addadi zai kai kashi 1 cikin 4 na jama´ar dake fama da talauci a Jamus.
Saidai ayar tambaya a nan itace, mine ma´auyin talauci a wannan ƙasa ta dake matsayin jagoran ta fannin tattalin arziki a nahiyar Turai.
Fasara da hukumomin Jamus suka baiwa talauci, itace duk mutumen dake rayuwa a Jamus tare da ƙasa ga Euro 781 a wata, wato kimanin CFA jikka ɗari biyar, kokuma Naira dubu 140, ya na ga jerin matalauta.
Hukumomin Jamus sun yi na´ am da cewar wannan alƙaluma na talauci ba za su aiki ba idan aka kwatanta da yadda jama´a a wasu ƙasashe na duniya ke fama da fatara inji Hubertus Heil Sakatare Jannar na Jam´iyar SPD.
Ministan kyauttata rayuwar jama´a a gwamnatin Tarayya Host Seehofer ya ambata yiwuwar ƙayyade farashen Euro 7 da rabi ako wace awa ta aiki a wani mataki na rage yawan matalauta a Jamus.
A nata gefe Jam´iyar Links ta bayyana bukatar gwamnati ta dauki matakan inganataw ma´aikata ta yada mafi yawa daga cikin su, su sami a ko wane wata Euro kimanin dubu 3 da rabi , idan kuma akwai yara da suka kai biyu albashin ya zarta Euro dubu 7 wato fiye da CFA miliyan 4 ko kuma Naira miliyan ɗaya da ´yan ka.
Ranar 25 ga watan mai kamawa hukumar gwamnatin tarayya mai yaki da talauci da kuma kyautata rayuwar jama´a za ta zaman taro, domin dubna hanyoyin magance wannan matsala.