Duniya za ta karbi dubban jarirai a ranar farko ta 2020
January 1, 2020Majalisar ta Dinkin Duniya ta yi bikin murnar karbar sabbin jarirai dubu 392 haihuwar yau daya ga watan Janairun 2020 a fadin duniya.
Sai dai a share guda Majalisar ta Duniya ta ja hankalin kan yiwuwar da dama daga cikin jariran ka iya mutuwa kafin su kai shekaru biyar da haihuwa saboda matsaloli da kananan yaran ke gamuwa da su.
Wata kididdigar da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayar, na nunin cewa jarirai sabbin haihuwa miliyan biyu da dubu 500 suka mutu a shekarar 2018.
Kididdigar ta ce sun kuma mutu ne sakamakon matsalolin da ake iya kauce musu.
Indiya ce ke kan gaba a hasashen bana na sabbin haihuwa a ranar farko ta sabuwar shekarar da ake ganin za a iya samun yara dubu 67 da 385.
Kasar China ce ke biye mata da jarirai dubu 46 da 299; sai kuma Najeriya da ake sa ran a yau za a haifi jarirari dubu 26 da 39.