1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Turkiyya ta kori jakadun manyan kasashe

October 24, 2021

Gwamnatin Turkiyya, ta kori jakadun kasashen waje 10 da ke kasar ciki har da na kasashen Jamus da  Amirka. Jakadun sun bukaci a saki wani dan fafutika ne da ke tsare.

https://p.dw.com/p/426xh
Putin empfängt Erdogan in Sotschi
Hoto: Vladimir Smirnov/Sputnik/REUTERS

Matakin wanda ya zo kai tsaye daga Shugaba Recep Tayyip Erdogan a ranar Asabar, ya biyo kira ne da jakadun kasashen suka yi na a saki wani dan gwagwarmaya, Osman Kavala, da ke a tsare tsawon shekaru.

Jakadun sun bukaci sakin mutumin ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka rubuta a ranar Litinin, suna cewa ci gaba da tsare Osman Kavala, ya sanya shakku a kan gwamnatin Shugaba Erdogan.

Turkiyyar dai ta tsare Kavala ne tun a shekara ta 2017, saboda zargin sa da jagorantar zanga-zanga a 2013 da ma hannu a yunkurin kifar da gwamnati a shekara ta 2016.

Amirka dai ta ce tana sane da labarin, sai dai tana jiran karin haske daga ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya, yayin da Jamus ta ce tana tattaunawa da gwamnatocin kasashen da matakin ya shafa.