Turkiyya ta kara haraji kan kayayyakin Amirka
August 15, 2018Talla
Kasar Turkiyya ta sanar da tsananta haraji kan wasu kayayyakin da ke shigo wa kasarta daga Amirka, abin kuma da zai kara tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke nuna wa juna yatsa.
Turkiyyar dai ta ce ta kara harajin ne kan Motocin Amirka da shinkafa da makamashin kwal da kayan kwalliya gami da barasa.
Mataimakin shugaban kasar Fuat Oktay ya ce an yi hakan ne a matsayin ramuwa ga matakin da Amirka ta dauka kan kasar dangane da darajar kudin Turkiyya wato Lira.
Cikin 'yan makonnin na dai kudin Turkiyyar ya fadi da wani kaso idan aka kwatanta da dala, da ya shigar ta tattalin arzikin kasar cikin wani yanayi.
Masu saka jari dai na nuna damuwa kan tsare-tsaren tattalin arzikin kasar karkashin shugaba Racep Tayyip Erdogan.