1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsofin fursuna Guantanamo a Ghana

Jamila Ibrahim Mai Zongo/AHJanuary 7, 2016

An bai wa wasu mutane guda biyu da aka zarga a baya da laifin aiyyukan ta’addanci waɗanda ake tsare da su a Guantanamo BAY, da ke a Kyuba, mafaka a Ghana abin da kuma ya janyo martanin jama'ar ƙasar.

https://p.dw.com/p/1Ha09
Symbolbild Guantanamo
Hoto: Getty Images/J. Moore

Mutanen biyu dukkaninsu yan asilin ƙasar Saudiyya ne, amma ake yi musu kallon 'yan asalin ƙasar Yemen, ana sa ran isowarsu a ƙasar Ghana a ranar yau ɗin nan. Kuma sun haɗa ne da Khalid Mohammed Salih al-Dhuby, mai shekaru 38 da kuma Mahmmoud Omar Mohmmed Bin Atef, mai shekaru 36, wadanda ake tsare da su tun a shekarar 2002.

An aike da mutanen ne guda biyu zuwa Ghana saboda za a rufe Guantanamo

An dai tsaida shawarar tura mutanen ne zuwa ƙasar Ghana ne, bayan da majalisar dokokin Amurkar da ke tsare da su ta bayyana cewar ba ta buƙatar fursunonin na Guantamo Bay a ƙasar bayan da shugaban Amurkar Barack Obama ya bayyana aniyarsa ta rufe sansanin. Kuma ba za a iya aike da su ba zuwa ƙasar Yemen ɗin sakamakon rikice-rikicen addini da ƙasar take fama da shi. Felix Kwakye Ofosu shi ne mataimakin daraktar sadarwar gwamnatin Ghana.

Symbolbild Guantanamo
Hoto: Getty Images/J. Moore

''Muna ƙoƙarin saka duk matakan tsaro da suka cancanta. Kuma ina tunanin za mu yi haka ɗin ne domin tabbatar da tsaron jama'ar ƙasar tare kuma da tabbatar musu da cewar kasancewar waɗannan mutanen biyu a ƙasar ba zai haifar da wani cikas ba ta fuskar tsaro.''

Fargaban jama'a a kan ba da mafakar ga mutanen biyu

Ci gaba da tsare waɗannan mutane a ƙasar Ghana tsawon shekaru 2, tamkar ci gaba da tsarin ne na Guantanamo Bay , wanda kuma ƙasashen duniya ke kallo a matsayin kaucewa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma keta hakkin bil adama.Dokta Kwajo Apiagyei Atuah, babban malamin shari'a ne a jami'ar Ghana ta Legon.

Symbolbild Guantanamo
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Shephard

''Wannan wani matakin agaji ne na ƙasa da ƙasa. ba za'a tsaresu a Ghana ba a bisa san ransu. lallai ne sai da hukumomin tsaron Ghana suka tuntuɓesu kuma suka gama tantancesu, don haka ma akwai mutum na uku wanda ya ce baya san zuwa ƙasar Ghana kuma aka kyale shi.

Sai dai kawo yanzu jama'ar ƙasar ne ke ci gaba da tsokaci tare da nuna shakku a kan barazanar da ke tattare da wannan matakin, a yayin da yaƙi da aiyyukan ta'addanci ya zamo ruwan dare gama duniya.