Taron ministocin G20 a Bonn
February 16, 2017Ministocin harkokin waje na kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya G20, sun fara wata ganawa a wannan Alhamis a birnin Bonn na tarayyar Jamus don tsara hanyoyin tunkarar matsalolin da kasashen ke fuskanta musamman ma neman sanin alkiblar sabuwar gwamnatin Amirka kan dangantaka da kasashen.
Mai masaukin baki ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel, ya ce zaben Donald Trump da aka yi a Amirka wata matashiya ce ga kasashen Turai, muddin suna da bukatar shiryawa hangen matsalolin da ke gaba. Haka nan ya ce kasashen tarayyar Turai musamman na bukatar sauye-sauye idan har tana son kasashe irinsu Amirka da Rasha da kuma China su dauke su da gaske.
Sigma Bagriel ya kuma ce lallai ne sai sun mike, ko da kuwa ta karfin soja ne, don ganin sun yi tazara daga dogaro kan goyon baya daga Amirka. Taron dai zai dubi batutuwan dorewar muradun ci gada na duniya da kasashe suka aminta da su nan da shekara ta 2030, gami da tsara hanyoyin tallafawa kasashen nahiyar Afirka.