Taron G7 zai samar da miliyoyin yaki da gobarar Amazon
August 26, 2019Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce taron kasashen nan bakwai ya dau hanyar kauce wa samun rigima dangane da shirin nan na nukiliyar Iran.
Yayin wata ganawa da 'yan jarida a taron kasashen a Faransa, Angela Merkel ta ce bakin shugabanni ya zo daya kan cewa Iran ba za mallaki makaman nukiliya ba, kuma Amirka ta yi marhabin da shirin tattaunawa tsakanin kasashen Turai da Iran.
A share guda kuwa, shugabannin kasashen sun amince da samar da euro miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 22, don taimaka wa yaki da gobarar nan da ke cin kungurmin dajin nan na Amazon.
Kaso mafi tsoka daga kudaden dai, za su tafi ne wajen aikawa da jiragen da za su gudanar da aikin kashe wutar, a cewar wata majiya daga fadar shugaban kasar Faransa.