1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta yanke kauna da wakilin Majalisar Dinkin Duniya

June 9, 2023

Gwamnatin mulkin soja a Sudan, ta zargi wakili na musamman na MDD dan asalin Jamus da kara rura watar rikicin da kasar ke ciki. Ta ce ta ma sanar da Antonio Guterres batun.

https://p.dw.com/p/4SMXj
 Volker Perthes
Hoto: Eskinder Debebe/UN Photo/Xinhua/picture alliance

Shugaban gwamnatin mulkin soja a Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya zargi wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya dan asalin kasar Jamus, Volker Perthes da kara rura watar rikicin da kasar ke ciki.

Ma'aikatar kula da al'amuran kasashen ketare a Sudan ta bayyana Volker Perths a matsayin mutumin da suka yanke kauna da shi.

Tuni ma dai aka sanar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, wannan lamari.

A tsakiyar watan Afrilun da ya gabata ne dai sojojin kasar Sudan da kuma rundunar kar ta kwana ta RSF karkashin jagorancin tshohon mataimakin shugaban kasa Mohamad Hamdan Daglo suka fara kai wa juna hare-hare.

Bangarorin na yaki ne musamman a Khartoum babban birnin kasar, da kuma yammacin yankin Darfur.

Bangarorin sun kuma yi ta saba yarjeniyoyin tsagaita bude wa juna wuta da suka cimma.