Steinmeier: Ci gabanmu na hannunmu
December 25, 2018Talla
A sakonsa na musamman albarkacin bikin Kirsimetin bana, Shugaba Frank-Walter Steinmeier ya ce ba zai yiwu kasar ta rabe saboda wata 'yar rashin fahimta ba.
Shugaba Steinmeier ya ce galibin mutane na fifita abin da suke so ne ta hanyar wofinta duk abin da wasu suka yarda da shi a kullum.
Jamusawa a cewar shugaban kasa ba su yawaita yi wa juna magana ko uzuri, yana mai jaddada cewa dukkanin al'umar kasar mutane daya ne, koda kuwa daga ina suka fito ko yanayin launin fata ko kuma abin da suke ra'ayi.
Bambance-bambancen siyasa ko zamantakewa a Jamus dai sun karu cikin wannan shekarar ta 2018 da ke shirin ban-kwana, inda wasu ke ta nuna fushinsu ta shafukan sada zumunta maimakon zama don warware su cikin girma da arziki.