Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea Conakry
September 5, 2021Talla
Wani faifan bidiyo ya nuna Laftanal Kanal Doumbouya, Zagaye da wasu sojojin, na cewa sun yanke shawarar jingine kundin tsarin mulki tare da tabbatar da kame shugaban kasar.
"Yace mun jingine kundin tsarin mulki, za mu dakatar da ayyukan hukumomin gwamnati sannan za mu rusa majalisar zartarwar gwamnati. Tare da hadin gwiwar dukkanin dakaru, za mu samo hanyar warware matsalolin da suka yi wa kasar nan dabaibayi."
Su dai sojojin da suka sanar da kame shugaba Alpha Conde, sun ce tuni suka rufe iyakokin kasar na sama da kuma na kasa, baya ga dakatar da harkokin gwamnati.
Kasar ta Guinea da ke cikin jerin kasashe matalauta na duniya, wadda kuma ke alfahari da dumbin albarkatun karkashin kasa, ta kwashe shekaru tana fama da rashin daidaiton siyasa.