1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar siyasar Chadi tare da sojoji

September 30, 2022

Bangarorin siyasa a Chadi na cece-kuce kan shawarwarin da wani kwamiti ya bayar na ganin jagororin gwamnatin mulkin sojan kasar sun tsaya takara a zaben kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4HaXY
Taron nemar wa Chadi mafita a siyasance
Taron nemar wa Chadi mafita a siyasanceHoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

Ko baya ga takarar shugaban gwamnatin mulkin soja ta rikon kwarya Mahamat Idriss Déby Itno, kwamitin ya kuma bukaci da sojojin su ci gaba da tafiyar da mulki har nan zuwa wasu watanni 24 kafin a shirya zabe.

Kura ta bude babban taron koli na tattauna al'amurran siyasa da alkiblar Chadi bayan da wani kwamiti ya shigar da bukatar ganin an bai wa sojan da ke rike da mulki damar tsayawa takarar mukaman siyasa. Wasu na ganin matakin ya zo daidai gabar da ake bukata, a yayin da ake dab da jan labulen babban taron kolin na Chadi. Sai dai ga wasu, batun ya zo masu a karkace duba da wasu alkawuran da sojan da ke mulki suka yi ciki har da na kin tsayawa takara a manyan zabukan kasar.

Shugaban sojoji na rikon kwarya a Chadi Mahamat Idriss Deby
Shugaban sojoji na rikon kwarya a Chadi Mahamat Idriss DebyHoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

To amma ga tsohon madugun 'yan adawa Saleh Kebzabo da ke zama mataimakin shugaban kwamitin taron kolin na Chadi kwamitin ya yi gagrumin aikin da za a iya yabawa masa. Madugun 'yan adawar dai na dora alhakin makomar Chadi kan wadanda suka kaurace wa taron.

Sai dai kafin wannan lokaci, ga wasu gungun kawancen jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula na Wakit Tama, tanadin da kwamitin ya yi ba abin mamaki ba ne in ji Max Loanlgar kakakin kawancen.

" Ga kawancen 'yan adawa na Wakit Tama tuni mukasan a rina tun a gabanin soma taron, bisa take-taken da muka lura sojojin da ke mulki na yi na makalewa kan iko." in ji  Loanlga

Karin bayani: Yiwuwar shigar sojoji cikin siyasar Chadi

Jam'iyyun siyasa da dama da kawancen kungiyoyin kare dimukuradiyya sun kaurace wa taron tun daga farko, kana shawarwarin da kwamitin ya bayar na tsayawa takarar sojan da ke mulki na shan suka. Ko ma dai kakakin wani kawancen da ke fafutikar ganin an gudanar da taron a cikin tsanaki Bedoumra Kordjé, da yake zantawa da DW cewa ya yi matakin baya da wani tushe a tsarin kungiyar AU domin kuwa ta riga ta nuna adawarta da takarar sojan da suka karbi ragamar mulki bayan mutuwar Deby. Sai dai kakakin jam'iyyar MPS ta marigayi Idriss Deby Itno Jean Bernard Padaré ya musanta zancen, inda ya ce, ''ba wata ayar dokar da ta hana sojan da ke mulki tsayawa takara a Chadi.''

Karin bayani: Shawarar ci gaba da wa'adin mulki

Duk da yake masu adawa a Chadin na da yakinin cewa ba a kifar da wata gwamnati ba a kasar, ci gaba da rike mulki daga bangaren soja ne ya sabawa ka'ida.

Kwamitin dai da ya bukaci Mahamat Idriss Déby Itno ya tsaya takara, ya kuma shigar da bukatar ganin wa'adin mulkin kasar ya kasance na tsawon shekaru 6 har sau biyu, ba tare da wani hurumi na sake ayar dokar ba domin zarcewa idan har an zabi sabon shugaban kasa na tafarkin dimukuradiyya.