1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: 'Yan siyasa na adawa da shigar sojoji siyasa

Blaise Dariustone AMA/ZUD
September 29, 2022

Ana shakkun ko sojojin da ke rikon mulkin Chadi ka iya tsayawa takara a zaben kasar da ke tafe. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da taron koli kan shugabanci ke tsara yadda kasar za ta koma mulkin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/4HWio
Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta sojoji a Chadi Mahamat Idriss Déby
Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta sojoji a Chadi Mahamat Idriss DébyHoto: Facebook.com/Präsidentschaft der Republik Tschad

Karamin kwamitin da aka dora wa alhakin nazari kan makomar jagororin siyasar kasar ya ce ba wata ayar dokar da ta hana kowanne jigo a majalisar koli ta rikon kwarya a gwamnatin mulkin soji da ya tsaya takara a zabe. Kwamitin ya kara da cewa duk wani kusa a gwamnatin mulkin soja ka iya tsayawa takara madamar ya cika ka'idojin da dokoki suka tanada a matsayinsa na dan kasa.

Kakakin kwamitin Dokta Robenate Jean Calvin ya kuma bayyana cewa batun tsarin taswirar mulkin da ake son dora Chadi a kai ya danganta ne kan zaben raba gardama da ake son al'umma ta kada kuri'a a kai. Sai dai taron tattaunawar keke-da-keke da ake shirin yanke komawa a Alhamis din nan ne kadai ka iya cewa wani abu game da wadannan jerin bukatu.

 Bude taron koli kan rikicin shugabancin Chadi a watan Agusta na 2022 a N'Djamena
Bude taron koli kan rikicin shugabancin Chadi a watan Agusta na 2022 a N'DjamenaHoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

Masu sharhi kan harkokin siyasar Chadi irinsu Kebir Mahamat Abdoulaye tuni suka fara sukar lamarin.

"Za mu zura ido mu gani me mahalarta taron za su ce game da wannan batu. Za mu jira kuma mu ga me za su ce game da taswirar tsarin tafiyar da mulki." in ji Abdoulaye

Kafin sake komawa kan zauren muhawarar dai da dama sun fara tofin Allah tsine kan batun na tsayawa takarar sojojin da ke mulki, musamman Shugaba Mahammat Idriss Deby da ke kan karagar mulki yau watanni 16 ke nan da suka gabata.

Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta sojoji a Chadi Mahamat Idriss Déby
Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta sojoji a Chadi Mahamat Idriss DébyHoto: Michel Euler/AP Photo/picture alliance

Ko baya ga batun bai wa shugabannin Majalisar Koli ta Mulkin Sojan damar tsayawa takara, batun kara wa'adin mulki har na tsawon shekaru biyu na daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin kwamitin, inda yake fatan ganin sojojin sun tsawaita wa'adin mulkinsu har nan da wasu watanni 24 da ke tafe bayan sun shafe watanni 16 kan madafan iko.

Ana dai sa ran Mahamat Idriss Deby zai ci gaba da rike mukaminsa na shugaban riko ne maimakon matsayinsa na yanzu na shugaban Majalisar Mulkin Soja ta Rikon Kwarya.