1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Rasha ba zai halarci taron G20 ba

November 13, 2022

Ta tabbata cewa Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ba zai halarci taron kasashe masu karfin tattalin arziki da za a yi a kasar Indonesiya ba. Tuni ma ya aika da wakili a taron na G20.

https://p.dw.com/p/4JSJo
Shugaba Vladimir Putin na RashaHoto: Mikhail Metzel/Sputnik/dpa/picture alliance

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya isa tsibirin Bali na kasar Indonesiya inda zai halarci taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a madadin Shugaba Vladimir Putin wanda ba zai halarta ba. Babban jami'in diflomasiyyar Rashar wanda ya samu tarba ta girmamawa daga wasu masu rawan gargajiya, ana sa ran zai fuskanci suka daga taron saboda mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, da ma barazanar amfani da makaman nukiliya a rikicin.

Sergei Lavrov din ne zai jagoranci taron manyan kasashen na duniya a Indonesiya, wanda shi ne kuma na farko da ake yi tun bayan afka wa Ukraine da yaki a cikin watan Fabrairu. Ita dai Rasha tana ci gaba da kiran abin da take yi a Ukraine a matsayin wani sintiri na musamman.