Shugaban kasar Jamus ya yi kiran hadin kai
November 20, 2018Talla
Mr. Steinmeier wanda ya yi gargadi kan yadda wasu ke rikon tsananin ra'ayin kishin kasa, ya ce lallai ne kasashe su hada kai domin iya shawo kan manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.
Shugaban na Jamus ya nuna bukatar hakan ne a kasar Afirka ta Kudu inda yake ziyarar kwanaki uku.
A jawabin da ya gabatar a gidan adana tarihi na mulkin wariyar launin fata da ke birnin Johannesburg, Shugaba Steinmeier, ya ce kasancewar Jamus da Afirka ta Kudun mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, zai dace kasashen biyu su yi amfani da damar wajen aiki tare.
Afirka ta Kudun dai ita ce kadai kasar Afirka da ke cikin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya.