SiyasaAfirka
Shugaban Faransa Macron na son kulla alaka da Diomaye Faye
March 30, 2024Talla
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shaidawa sabon zababben shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye cewa yana da muradin ci gaba da kulla alaka mai karfi tsakanin kasashen biyu.
Karin bayani:
Wannan dai nAU ta yi fatan nasara ga gwamnatin Diomaye na Senegala cikin sakon taya murna ta wayar tarho da Mr Macron ya aike wa sabon shugaban na Senegal, mai akidar yaki da cin hanci da rashawa da kuma sake fasalin kasar.
Karin bayani:Bassirou Diomaye Faye ya lashe zaben shugaban kasar Senegal
Fadar shugaban Faransa ta Elysee ta ce shugabannin biyu sun tattauna muhimman batutuwa kan yadda za su yaukaka alakar da ke tsakaninsu.