AU ta yi fatan nasara ga gwamnatin Diomaye na Senegal
March 29, 2024Sakon taya murnar AU na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar mai barin gado Macky Sall ya karbi bakuncin shugaban kasar mai jiran gado Bassirou Diomaye Faye da madugun adawa Ousmane SONKO a fadar gwamnatin Dakar.
Karin bayani: 'Yan takarar shugaban kasa a Senegal sun kaddamar da yakin zabe
Shugabannin sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi makomar ci gaban kasar ta Senegal tare da cimma matsaya kan batun shirye-shiryen mika mulki da ake sa rai a ranar 2 ga watan Afrilun wannan shekara.
Karin bayani: Senegal: Sonko da Diomaye sun shaki iskar 'yanci
Diomaye Faye wanda bai taba rike mukamin siyasa ba shi ne shugaba na biyar da zai mulki kasar tun bayan samun 'yancin kasar tun daga lokacin Leopold Sedar Senghor da Abdou Diouf da Abdoulaye Wade sai kuma Macky Sall mai barin gado.