Shugaba Erdogan zai ziyarci Jamus
November 11, 2023A yayin wannan ziyara da ke zama ta farko da Recep Tayyip Erdogan zai kawo Jamus cikin shekaru uku, shugaban zai gana da shugaban gwamnatin Olaf Scholz a ranar Juma'a mai zuwa kamar yadda kakakin gwamnatin ta Berlin ta tabbatar.
Karin bayani: Erdogan ya soki sabon rikicin Gabas ta Tsakiya
Wannan ziyara dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Turkiyya da membobin NATO a game da rikicin Isra'ila da Hamas wanda ya barke kwanaki 35 da suka gabata.
Tattaunawar shugabannin biyu za ta mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda kakakin gwamnatin Jamus ta shaida wa manema labarai.
Karin bayani: Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra'ila, tare da yanke duk wata hulda da Firminista Benjamin Netanyahu
A baya dai mista Erdogan ya kakkausar suka ga Isra'ila tare da zarginta da aikata laifukan cin zarafin bil adama a zirin Gaza inda ya kirayi jakadan Turkiyya daga kasar don nuna bacin ransa.