1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban Turkiyya ya soki rikicin Gabas ta Tsakiya

Zainab Mohammed Abubakar MNA
October 11, 2023

Turkiyya ta yi Allah wadai da kisan fararen hula a Isra'ila amma kuma tana adawa da hare-haren wuce gona da iri a kan Gaza, in ji shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan.

https://p.dw.com/p/4XPYb
Recep Tayyip ErdoganHoto: AFP

A taron jam'iyyarsa Erdorgan ya ce "Muna adawa da kashe fararen hula a yankunan Isra'ila a fili, a lokaci guda kuma, ba za mu taba amincewa da kisan gillar da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza, ta hanyar kai hare-hare".

A cewarsa dai wannan  ba yaki ba ne, kisan kiyashi ne a lokacin rikici ta hanyar amfani da kowane nau'i a kan jama'a.

Shugaban Turkiyyan ya ce Isra'ila na hana mutanen Gaza kayayyakin agaji na bukatun yau da kullum da suka hada da ruwa da wutar lantarki, yayin da suke kai hari kan ababen more rayuwa da wuraren ibada da kuma makarantu.