Cikin shirin za a ji Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague ICC, ta yi kiran kawo karshen rikicin da ke wakana a yankin zirin Gaza. Cikin wata sanarwar da ta fitar, babbar mai gabatar da kara Fatou Bensouda, ta ce kisar falasdinawa 29 da dakarun Isra'ila cikin makonni biyun da suka gabata, na iya fuskatar bincike daga ofishinta.