Cikin shirin za a ji Shugaban Amirka Donald Trump ya yi kiran hadin kan Amirkawa tare da tabbatar da tsare martaba da iyakokin kasar. Shugaban na Amirka ya kuma tabbatar da matsayin Amirkar kan janye tallafin da ta ke bai wa kasashe da ya bayyana da makiyan Amirkar, bayan kin amince wa matsayi kan birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.