Kalubalen mata manoma a kasar Senegal
September 28, 2023Duk da yake akwai dokoki da suka tanadi daidaito tsakanin maza da mata na samun filaye a Senegal, amma a zahiri mata musamman a yankunan karkara suna samun filayen ne sannu a hankali abin da ake gani tamkar juyin-juya hali saboda matsalolin al'adu. Tening Sene tana jagoranci wata kungiya mai saka ayar tambaya kan mtsalolin na mata, duk da yanayin da ake ciki. Tana aiki tare da taimakon 'yarta kuma ta gamsar da mijinta ya sake mata gona mbabba, inda mata kimanin 40 suke aiki a ciki.
Wannan ya zama wata alamar nasara ga matan kasar ta Senegal, inda kaso 15 cikin 100 ne kacal suka mallaki filin noma a cewar Hukumar Kula da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya. A bisa al'ada maza suke gadon gonaki daga maza, mata ba su da wata hanyar sauya tsarin musamman saboda karancin bayanan da doka ke bukata. Domin ganin matan yankunan karkara sun dogara da kansu ta fannin tattalin arziki a Senegal, kungiyoyin fafutuka na kara nuna tasirin aikin gona da yadda mutane suka dogara a kai musamman a yankunan karkara tare da nuna tirjiya kan mika gonakin ga manyan kamfanoni. Matan dai na ci gaba da nuna fata na samun karin gonaki, abin da zai karfafa musu hanyoyin samun kudin shiga.