1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Senegal Macky Sall ya jingine tazarce

Mouhamadou Awal Balarabe
July 4, 2023

Bayan shakku na tsawon lokaci, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya kawo karshen ya katse zarginsa da neman yin tazarce a wani wa'adi na uku kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/4TOxK
Macky Sall shugaban kasar Senegal
Shugaban kasar Senegal, Macky Sall Hoto: Lewis Joly/AP/picture alliance

A jawabin da ya yi wa 'yan kasa ya ce ba zai yi takara a zaben a watan Fabrairun 2024 ba. Amma tsawon lokaci da ya dauka kafin ya bayyana matsayin kan takarar ya haifar da martani irin daban-daban a tsakanin 'yan siyasa da 'yan farar hula na Senegal.

Wannan sanarwa da aka dade ana jira, ta kawo karshen tsama da ake yi tsakanin shugaban da ke kan karagar mulki tun 2012 da 'yan adawa da ke zarginshi da yunkurin neman yin tarazce bayan wa'adi biyu.

"Sabanin jita-jita da ke danganta ni da marar burin neman sabon wa'adi na shugabancin kasa, ina so in jaddada muku cewa ina sane kuma ina tunawa da abin da na fada na rubuta kuma naa maimaita a nan kasar da sauran wurare, wato wa'adin 2019 ya kasance zango na mulki na biyu kuma na karshe."

Akasarin 'yan siyasa na Senegal sun yi maraba da wannan shawarar ta Sall ta kin sake tsayawa takara, wacce suka bayyana a matsayin mai hikima, wacce kuma za ta dawo da martabar dimokuradiyyar Senegal da ta sukurkuce a baya-bayan nan saboda jan kafa da Macky Sall ya yi wajen bayyana aniyarsa. Amma Mamadou Mbodj da ke zama shugaban F24, har yanzu akwai sauran rina a kaba domin yana cike da damuwa kan tashe-tashen hankula.

Madugun adawa Ousmane Sonko
Ousmane Sonko, madugun adawa a SenegalHoto: Fatma Esma Arslan/AA/picture alliance

"A cikin wannan jawabi, ya fi maida hankali a kan tashe-tashen hankula da aka fuskanta, ya yi zargi wasu a koda yaushe da ruruta wutar rikici, alhali da duk tashe-tashen hankulan da ke faruwa a kasar nan suna da alaka da hukumomi da cin zarafi na danniya."

Da farko dai madugun adawa Ousmane Sonko ya yi kira ga 'yan Senegal da su gudanar da gagarumar zanga-zanga domin kalubalantar Macky Sall idan ya sake tsayawa takar. Amma shugaban dandalin kyautata zamantakewa a Senegal Mamadou Mignane Diouf ya ce wannan shawarar da shugaban kasar Macky Sall ya yanke za ta taimaka wajen rage tashin hankali a fagen siyasar kasar. Amma abin jira a ganinsa, shi ne ruwan sanyi da kotun Senegal za ta yayyafa a shari'o'in siyasa da suka shafi mutane da yawa ciki har da madugun adawa Ousmane Sonko.

" Ya kamata mahukuntan Senegal da alkalan kasar su yi kokarin ganin yadda za su bi hanyar warware rikicin siyasa da na shari'a  da sauran rikice-rikice da shari'a ke ba da gudummawar haddasawa, don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samar da sulhu bisa sakamakon da aka samu a tattaunawar kasa da aka yi kwanan nan."

'Yan adawa na zanga-zangar kin jinin tazarce a Dakar
Duban magoya bayan 'yan adawa na zanga-zangar kin jinin tazarce a DakarHoto: Sylvain Cherkaoui/AP/picture alliance

Bayan da aka kawo karshen tazarcen Macky Sall, akwai wasu matsaloli da 'yan Senegal ke fatan ganin an warware su, ciki har da sakin fursunonin siyasa da kuma sauya makomar Ousmane Sonko, shugaban jam'iyar Pastef da aka yankewa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari saboda zargin tunzura matasa ga yin bore, lamarin da ka iya hana shi tsayawa takara idan dai ba a yi yafiya ba.

Amma a cikin jawabinsa, Shugaba Macky Sall ya yi alkawarin bin diddigin tashe-tashen hankula da suka wakana a Senegal, inda ya ce za a gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika da masu daukar nauyinsu da kuma wadanda suka mara musu baya.