Sama da yara dubu 10 sun mutu
June 28, 2018Wani rahoton da MDD ta fitar, ya ce sama da kananan yara dubu 10 ne aka tabbatar da cewa sun salwanta, a rikice-rikicen da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya cikin shekarar da ta gabata kadai. Baya ga wadanda suka mutun, akwai ma wasu dubban da aka ci wa zarafi ta hanyar fyade da kuma tilasta masu zama sojoji duk da karancin shekarun nasu. Rahoton ya ce sama da yara dubu 21 ne suka fuskanci tsananin cin zarafin, alkaluman da suka zarta na shekarar 2016, a yankunan kasashen da ke fama da yake-yake.
Majalisar ta Dinkin Duniya dai ta dora laifi kan Amirka wadda ke mara wa wasu bangarori da ke yaki cikin kasashen Larabawa, musamman ma kasar Yemen da aka yi asarar rayukan kananan yara sama dubu da 300 a baran. Yaran da ke aikin yaki a Yemen da ma wasu kasashen a cewar rahoton sun kama daga shekaru 11 da haihuwa.