1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fara nada ministocin Kenya

Suleiman Babayo ZUD
July 19, 2024

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya nada bangaren farko na mutane 11 a matsayin sabbin ministocin kasar yayin da yake ci gaba da tattaunawa domin samar da daukacin ministocin.

https://p.dw.com/p/4iWi3
Kenya Nairobi Shugaba William Ruto Taron Manema Labarai
Shugaba William Ruto na KenyaHoto: TONY KARUMBA/AFP

Shugaba William Ruto na kasar Kenya ya nada bangaren farko na mutane 11 a matsayin sabbin ministoci, cikin matakan neman kawo karshen zanga-zangar da gwamnatinsa take fuskanta. Lokacin jawabi ta tashar talabijin shugaban ya bayyana sunayen sabbin ministoci 11 gami da ma'aikatun da za su jagoranta.

Karin Bayani: Arangama ta barke a Kenya tsakanin 'yan sanda da matasa

Kasar ta Kenya da ke yankin gabashin Afirka ta shafe wata cikin yanayin zanga-zanga na adawa da kudirin kara haraji da neman kawo karshen cin hanci da rashawa. Sai dai bangaren adawa na kasar ya yi watsi da tayin shiga sabuwar majalisar ministocin. 'Yan adawa sun kira matakin Shugaba Ruto na garambawul ga majalisar ministocin a matsayin kwaskwarima, akwai dai ministocin da aka sake nadawa daga cikin wadanda aka rusa.

Kimanin mutane 50 suka yi imanin sun halaka lokacin zanga-zangar na kasar ta Kenya, sannan wasu fiye da 410 suka jikata, kamar yadda hukumar kare hakkin dan Adam na kasar ta bayyana.